Shiga (original) (raw)
Yadda masana’antar mutum-mutumi ke amfanar da tattalin arzikin kasar Sin
Masana'antar kera mutum-mutumi ta kasar Sin tana ci gaba da samun tagomashi tare da haifar da da mai ido ga ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, musamman ganin yadda ta samu ci gaba mai inganci a shekarar 2024. Ya zuwa karshen shekarar 2024, kamfanonin da ke kera mutum-mutumin da ake tasaruffi da su a bangarorin aikace-aikace daban-daban na kasar Sin sun kai yawan 451,700, inda jarinsu ya kai yuan triliyan 6.44 (kimanin dalar Amurka biliyan 880), kamar yadda bayanai daga hukumar daidaita harkokin kasuwanni ta kasar suka nunar.
12-Feb-2025